A`isha Allah ya kara yarda da ita tana ambatar: cewa maniyyin janaba ya kasance yana shafar tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi, wani lokacin yana kasancewa danye sai ta wankeshi daga tufafin da ruwa, sai ya fita zuwa salla, alhalin ruwan bai gama bushewa daga tufafin ba, wani lokacin daban kuma, maniyyin yana kasancewa busashshe, a wannan lokacin sai ta kankare shi daga tufafin nashi kankarewa, sai yayi salla a cikinsa.