Daga Abu Qatada Al-ansari -Allah ya yarda da shi- ya ce: Mun fita tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zuwa yakin Hunain- sai ya faxi Qissar sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya kashe wani (a wajen yaqi) yana da kayansa da abun da yake tare da shi na ganima" Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi