explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga miji ya zo wa matarsa ta duburarta; cewa shi tsinanne ne abin korewa daga rahamar Allah, kuma shi babban laifi ne cikin manyan laifuka.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Haramcin zakkewa mata ta duburarsu.
  • Jin daɗi daga mata a koma bayan duburarta na jikinta ya halatta.
  • Musulmi yana zakkewa mace ne ta farjinta kamar yadda Allah Ya umarce shi; amma ta dubura to a cikin hakan akwai ɓata ɗabi'a, da tozarta zuriya, da saɓawa abinda nagartattun ɗabi'u suke a kansa, da kuma cutuka masu kaiwa ga ma'auratan.