Nana aisha da Ummu Salama Suna Bamu labari cewa Annabi ya kasance yana tarawa da iyalinsa cikin dare, wani lokaci ma Asuba tana riskassa a halin yana cikin Janaba baiyi wanka ba kuma ya cika Azuminsa kuma baya ramawa, kuma ya kasance ya basu Labari ne sabida bawa Marwan Dan Hakam Amsa lokacin da ya aiko musu da tambayar; don ya tambayesu hakan. kuma wannan Hukunci cikin watan Azumi ne da waninsa ma.