Idan Allah yayi nufin Mutuwar Bawa daga cikin Bayinsa a Wata Qasa ta Musamman baya cikin ta, sai Allah ya sanya masa Buqata a wannan Qasar, kuma idan ya tafi buqatar tasa a wannan Qasa sai Allah ya karvi ransa, da kuma abunda Allah ya Qaddara kuma ya rubuta Masa babu makawa sai ya faru gare shi kamar yadda ya Qaddara shi, kuma wannan yana daga cikin Imani da Hukuncin Allah da Qaddara