Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa jikokinsa biyu Alhassan da Alhussain 'ya'yan Ali ɗan Abu Ɗalib da Faɗima 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma Allah Ya yarda da su -, su ne shugabannin wanda ya mutu a falala alhali shi yana saurayi kuma ya shiga aljanna, ko cewa sune shugabannin matasan 'yan aljanna in an cere Annabawa da Khalifofi Masu shiryarwa.