An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu" kuma na rantse da wanda Ran Abuhuraira ya ke a Hannunsa ba don Jihadi a tafarkin Allah ba da kuma Hajji, da kuma biyayyar Mahaifiyata ba, da nai kwadayin na Mutu ina Bawa Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
explain-icon

Explanação

Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah ya ce: "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu"; saboda tsayuwa da hakkin Allah Madaukakin Sarki- na ibadu da tsayuwarsa da hakkin Maigidansa na Hidima, Sannan Abuhuraira -Allah ya yarda da shi- ya bada labarin cewa ba don babu Jahadi akan Bawa ba, da kuma tsayuwarsa ga Hidimar Mahaifiyarsa na ciyarwa da Hidima wallahi da na fi son in zamanto na Mutu a Matsayin yana Bawa sabida Ladan da yake cikinsa