Qarshen ganin da Anas -Allah ya yarda da shi yayiwa Manzon Allah SAW shi ne lokacin da ya buxe labulen da yake tsakanin Xakinsa da Masallaci sai yaga Mutane sunyi Sahu suna Sallah a bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi- sai Abubakar ya zaci cewa Manzon Allah SAW futowa Sallah zai yi sai ya so ya dawo baya, don Manzon Allah yazo ya ja, sai yayi masa nuni da yayi zamansa, sai ya saki labulen kuma, kuma yayi Wafati a wannan Ranar kuma ita ce ranar litinin