Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana so kuma yana fifita cewa ya fara da dama a al'amuransa masu dacewa da girmamawa, daga cikin hakan: Ya fara da kafar dama a sanya takalminsa, kuma yana farawa da dama a taje gashin kansa da gemunsa a tajesu da shafa musu mai, a alwalarsa kuma yana gabatar da dama akan hagu daga hannaye da kafafuwa.