Lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah ya hana maza sanya alhariri sai dai a inda aka kebance, watau y'an yatsu biyu da aka ambata cikin hadisin Buhari da Muslim da ya gabata da kuma ruwayar Muslim da ta kara da cewa: ko uku ko hudu, don haka sai a yi amfani da mafi yawa, shi ne gwargwadon yatsu hudu ba laifi. ka duba Littafin Taasisil'Ahkam