Yusuf yana bada labari a cikin wannan Hadisin cewa Abdullahi Bn Salam -Allah ya yarda da su cewa Manzon Allah SAW ya sanya masa Yusuf kuma ya zaunar da shikan cinyarsa, kuma wannan yana daga cikin kyawawan Halayen Manzon Allah SAW da kuma Tawalu'unsa da jin qansa ga Yara.