Sun kasance suna dorawa bayi mata haraji, harajin da suke biyansa ta hanyar fajirci, kuma suna iya baiwa wanda ya yi zinar da su dan in ya nemi hakan. Sai Utbata Dan Abi Wakkas yayi lalata da baiwar Zam'ata Dan Al'aswad, sai baiwayr ta zo da yaron, sai Utbata yayi wasici ga Dan'uwansa Sa'ad da ya riskar da yaron zuwa ga kanshi. Bayan an yi Fatahu Makka, da Sa'ad ya ga yaron sai ya gane shi saboda kama da yayi da Dan'uwansa, sai yaso ya riskar da shi da Dan'uwansa, sai suka yi husuma da shi Abdu Dan Zam'ata, sai Sa'ad ya kawo hujjarsa inda yake cewa: Lallai Dan'uwansa ya tabbatar da cewa dansa ne,kuma ga kamanni nan ma, sai Abdu Dan Zam'ata yace: shi Dan'uwa na ne, Da ne daga cikin 'ya'yan Baba na, yana nufin: Babansa shi ne Uban gidan baiwar da ta haifi yaron, kuma shi ne mamallakin baiwar. Sai Annabi ya kalli yaron, sai yaga sunyi kama da Utbata. Sai ya yanke hukuncin Da na Uwarsa ne, mazinaci kuma ya yi asara, ba shi da alaka da yaron; saboda asali zai bi wanda ya mallaki uwar ne kuma ya take ta ta hanya ingattacciya, duk da haka da Annabi yaga kamamnin yaron da utbata wajen Dan