A cikin wannan Hadisin akwai bayanin Falalar Yanta Mutum Musulmi. kuma duk wanda ya 'Yanta Wani Wuya kai kace ya 'Yanya baki dayansa daga Wuta, Kuma lallai cewa a cikin 'Yanta Wuyaye akwai tabbatar da daukaka ga Musulmai da gusar Kaskancin Bauta daga gare su.