Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu mutane ba za su taɓa gushewa ba daga al'ummata suna masu rinjaye akan mutane, masu rinjayar waɗanda suka saɓa musu, hakan har sai al'amarin Allah ya zo musu ta hanyar karɓar rayukansu a ƙarshen zamanin duniya kafin tashin alƙiyama.