An karvo daga Umar Al-juma'i -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon ALlah SAW ya ce: "Idan Allah yana son Al-kairi ga Bawa sai yayi anfani da shi kafin Mutuwarsa" sai wani daga cikin Mutane ya tambaye shi, ta yaya zai yi aiki da shi? sai ya ce: "Allah sai ya shirye shi zuwa aiki na gari kafin Mutuwarsa, sannan ya kavi rayuwarsa a kansa" Ingantacce ne - Ahmad ne ya rawaito shi