Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "Annabi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba,siai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci,sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokaci Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi