explain-icon

Explanação

Jundub ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari mun kusa balaga, ƙarfafa masu tsananin ƙarfi, sai muka san imani a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin mu koyi Alƙur'ani, sannan muka koyi Alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.

explain-icon

Das notas do Hadith

  • Bayanin cewa imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa.
  • Jeranta abin da ya fi kamata a lokacin tarbiyyar mai tasowa, da kuma kwaɗayi akan cika musu imani.
  • Alƙur'ani yana ƙara imani, kuma zuciya tana haskaka da shi, kuma ƙirji yana buɗewa da shi.