Manzo mai tsira da aminci ya bayyana cewa Rana da Wata suna daga cikin ayoyin Allah masu nuni akan kudurar Allah da hikimarsa, canjawarsu daga asalin yadda suke baya faruwa don rayuwa ko mutuwar wasu manyan mutane kamar yadda mutanen jahiliyya suke kudurcewa,abubuwanda kan afku a duniya basu da tasiri a kansu. kisifewar Rana ko Wata kan faru ne saboda tsoratar da bayi, don zunubansu haka kuma don su sabunta tubansu, don kuma su koma zuwa ga Allah Madaukaki. Don haka Manzo ya shiryar akan a tashi ayi salla da addu'a har su sami waraka su yaye. lallai ga Allah sururruka da jujjuyawar al'amura suke