Annabi tsira da amincin Allah ya umarci ladaninsa' Bilal da ya maimaita lafazin kiran salla sau bibbiyu don shi kairan salla sanarwace ga wanda ba su nan,amma banda kabbara a farkonta,hakanan kuma yinsa sau hurhudu ya tabbata,hakanan kuma yin kalmar tauhidi sau daya akarshe,haka nan ya tabbata yinta sau daidai,kamar yadda ya umarci Bilal ya yi ikama sau daidai, domin ita tunatar da wanda suke gurin ne,amma banda(takbir),da lafazin kad kamatissalatu"don maimaita su sau bibbiyu ya tabbata