Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ji hayaniyar masu rigima,a kofar gidansa,sai ya fito don ya yi musu hukunci a tsakanin su sai yace: Lallai Ni mutum ne kamar ku, ban san gaibu ba, bana bada labarin boyayyayun al'amura, ban san waye mai gaskiya ko makaryaci a cikinku ba, masu rigima sukan zo dan na yi hikunci a tsakaninsu,kuma hukunci na yana kasancewa ne akan abin da na ji daga kowane bangare, da rantsuwoyinsu, kuma yana iya kasancewa wani yafi wani iya magana sai na zaci shi ne mai gaskiya sai na bashi gaskiya,tare da cewa abokin fadan shi ne mai gaskiya, ku sani ina hukunci da abubuwan da suke bayyane ne ba da wanda suke boye ba, ba zai halarta haram ba, don haka duk wanda na bawa gaskiya alhali ya san shi ne marar gaskiya, to yasan cewa wani yanki na wuta ne na yanko masa, in ya so sai ya dauka ko ya bari, sakamakon hakan na komawa akansa, Allah na jiran azzalumai a madakata