Manzon Allah SAW- yana cewa wannan sahabin zai yi tsawon rai har sai ya fahimci mutanen da suka saba wa koyarwarsa - SAW- a cikin gemun da ke samar da shi da kuma girmama shi zuwa wasa da ita , ta Hanyar da zasu rika kamanceceniya da Baubaye ko ma'abota wasa ko Ma'abota kece raini da Dukiya da kuma karairaya kuma suna keta akidar tauhidi ta hanyar amfani da hanyoyin shirka, kuma suna sanya abun wuya ko suna sanyawa Dabbobinsui, kuma suna neman amfani da haramtattun abubuwa. Ko kuma su aikata abin da annabinsu ya hana su na yin tsarki da kashin Dabbobi. Annabi -SAW- ya yi Wasiyya ga sahabinsa da su isar ga Alumma cewa annabin nata ba ruwansa da wadanda yayi wani abu daga hakan.