Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Kada ku kuskura ku tari gaban watan Ramalan da yin Azumin kwana daya ko kwana biyu, sai dai in Mutumin da ya saba yin wani Azumi to babu laifi don ya azumci lokacin.
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi