Mai-Shari'a Mai-Hikima ya hana Mai-Hukunci yayi Hukunci tsakanin Mutum Biyu alhali yana Mai-Fushi:Domin cewa Fushi yana tasiri abisa Ma'aunin Mutuntakar Mutum saboda haka ba'a amince ya zalunci ko ya kuskurewa gaskiya ba cikin Halin Fushinsa:sai hakan ya kasance zalunci abisa wanda Hukuncin ya hau kansa kuma Tabewa ga wanda yayi Hukunci da Zunubi akansa.