Babu wani Mutum da aka tava tsayar Masa da rana ba ta tsaya a falakinta sai Yusha'u Bin Nun kuma shi saurayi ne tare da Annabi Musa da yai tafiya tare da shi zuwa Khidhr lokacin da suka tafi Baitul Maqdis kuma cewa shi yaji tsoron faxuwar ta kafin ya shiga, kuma Ranar ta Kasance Jumu'a da ace ta faxi da ya shiga ne ranae Asabar kuma Yaqi a ranar haramun ne, sai ya ce da Rana ke Baiwar Allah ce nima haka, Ya Ubangiji ka tsayar da ita sai ta tsaya saboda shi har ya shiga Baitul maqdis