An rawaito daga Abu salama Bn Abdulrahman Bn Auf -Allah ya yarda da shi- cewa uwar Muminai Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce:Lallai Manzon Allah SAW ya nemi Auren Matansa yana mai cewa lallai ni yana baqantamun sha'aninku da rayuwarku yadda zata kasance bayan Mutuwa ta, saboda ban bar muku gado ba, kuma cewa babu mai iya haqurin ciyar da ku sai Masu haquri sannan Aisha ta ce da Abu salama Allah ya shayar da Mahaifinka Abdulrahman Bn Auf da ruwan Al-jannah wacce ake kira Salsabil kuma haqiqa yayi sadaka ha Matan Manzon Allah SAW da wata gona wacce aka sayar da iya kan kuxi da ya kai Dinare Dubu Arba'in