Kowane Jariri ana haifar sa sai Shaixan zai sokeshi a kuivinsa, sai ya kwalla kuka yayi Ihu bayan haihuwarsa kaxan saboda wannan zungurin na Shaxan, sai Maryam da Xanta Isa -Amincin Allah a garesu- saboda Allah ya kare su a lokacin haihuwarsu saboda Addu'ar Mahaifiyar Maryam lokacin da ta ce: "Kuma ni ina ne mata tsari da Zuriyarta daga Shaixan tsinanne" sai Allah ya amsa Addu'ar Mahaifiyar Maryam, sai ya kare Maryam da Xanta Isa daga zungurar Shaixan korarre ga barin rahamar Allah, Kuma babu wata Zariya ga Maryam in ba Isa -Amincin Allah a gare shi- kuma wannan Shafar ko sukar daga shaxan na haqiqa ne, kuma ba wai Ma'anarsa Kwaxayin Shaixan ba ne na vatar Xan Adam ba Kamar yadda Mu'atazilawa suke faxa, kuma ya wajaba ayi imani da hakan kan Haqiqaninsa, kamar yadda haka yake a Aqidar Ahlussunnah da jama'a