Share as Image
Share as Text
Add Explanation
Remove Explanation
Daga Umar Allah ya yarda da shi- cewa manzon Allah SAW ya ce: "Lallai cewa Allah yana daga Darajar wasu Mutane da wannan littafin kuma ya sauke Darajar wasu"
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi
Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata
Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma
Tir da xayansu da yake cewa Na manta Aya kaza da kaza, aa an mantar da shi ku riqa tuna Qur'ani, saboda shi ne mafi saurin mantawa daga zukatan Maza sama da Raquma
Kwatankwacin muminin da yake karanta AlKur'ani kamar gawasa ne, kanshinta mai dadi ne, kuma dandanonta mai dadi ne, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta AlKur'ani kamar dabino ne ba shi da kanshi amma dandanonsa ma zaki ne