An rawaito daga Kais Bn Abi Hazim, ya ce: Sayyadin Abubakar -Allah ya yarda da shi- ya shiga wajen wata Mata daga Kabilar Ahmas ana kiranta da Zainab, sai ya ganta bata Magana? Sa suka ce: tayi rantsuwar Hajji ne ba tare da Magana ba, sai ya ce da ita: kiyi maganarki, cewa hakan bai halatta ba, wannan yana daga cikin aikin Jahiliyya, sai tayi Maganarta. Ingantacce ne - Buhari ne ya rawaito shi