Daga Jubair Dan Mud'im -Allah ya yarda da shi- yace:"Na ji Annabi -tsira da amincin Allah- yana karanta Suratuddur a Sallar Magariba". Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
explain-icon

Explanation

Al'adar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana tsawaita karatu a sallar Asuba, ya takaita a Magariba, yayi tsakatsaki a sauran sallolin, amma wani lokacin sai ya bar abin daya saba yi don ya nuna halarci yin sabanin abin, kamar yadda ya zo a wannan hadisin cewa shi ya karanta "Waddur" kuma tana daga surorin da ake cewa {Diwalul Mufassal}