Daga Ibn Umar -Allah ya yarda da su- cewa manzon Allah SAW ya ce: Lallain Allah ya sanya Gaskiya a Harshen Umar da kuma Zuciyarsa" Kuma Ibn Umar ya ce: Babu wani abu da zai sauka ga Mutane su faxi wani abu a cikinsa, kuma Umar yace wani abu a cikinsa: sai Qur'ani ya sauka a cikinsa daidai da abunda umar ya ce Ingantacce ne - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi